A sa’I daya kuma tawagar "jiragen Somod" ta sanar da cewa ana gallazawa da dama daga cikin masu fafutukar a gidajen yarin Isra’ila, ciki har da mai fafutukar kare muhalli Greta Thunberg ta Sweden, wacce ta shiga cikin tawagar ta Somod Flotilla.
A cewar tawagar, daya daga cikin wadanda ake tsare da su ya ce: "An hana ni tsaftataccen ruwan sha, sannan sauran wadanda ake tsare da su ma an hana su magunguna masu muhimmanci".
Kungiyar gwagwarmayar ta Flotilla ta kara da cewa a cikin wata sanarwa da ta fitar ta ce har yanzu mambobi shida na cikin jirgin na hannun sojojin Isra'ila; Mutanen da a cewar kungiyar, an yi garkuwa da su ba bisa ka'ida ba a cikin ruwan kasa da kasa.
Your Comment